Jihar Enugu ,Jiha ce dake kudu-maso-gabashin Najeriya. Tana da iyaka daga bangaren arewa da jihar Benue da Kogi, jihar Ebonyi daga gabas, jihar Abia daga kudu, da kuma jihar Anambara daga yamma. Jihar ta samo sunanta ne daga Babban Birnin ta watau Birnin Enugu. Acikin, jihohi 36 dake Najeriya, Enugu itace ta 29 a fadin kasa kuma ita ce kuma ta 22 a yawan jama'a. Tana da yawan fili kimani na kilomita araba’i 7,161 da yawan jama’a milyan uku da dubu dari biyu da sittin da bakwai da dari takwas da talatin da bakwai (ƙidayar yawan jama'a shekara 2006). An ayyana yawan jama'arta a cikin shekara ta 2016 akalla mutum miliyan 4.4. Babban birnin tarayyar jahar ita ce Enugu. Ifeanyi Ugwuanyi shi ne gwamnan jihar tun zaben shekara ta 2015 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Cecilia Ezeilo. Dattijan jihar su ne: Gilbert Emeka Nnaji, Ike Ekweremadu da Utazi Godfrey Chukwuka.
© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search