Lagos (birni)

Legas island
Jihar lagos mai yawan jama'a
chunkoson jama'a a garin Lagos
Bene na farko a Nigeria wanda ke birnin Badagry a Lagos
Babban filin jirgin sama dake
Tinubu Square
Lagos wanda aka fi sani da "Murtala Muhammad International Airport"
Gabar Teku na Badagry wanda ke babban birnin Lagos
Babbab Asibitin EKO dake Victoria Island a Lagos
Tinubu Square

Birnin Legas, ko kuma Birnin Ikko, shi ne babban birnin Jihar Legas da ke Najeriya. Legas yana daya daga cikin birane mafi girma da yawan jama'a a Afirka da ma duniya baki daya. Legas ne birni na biyu mafi girma a Afirka, kuma na bakwai a duniya.[1] Kimanin mutum miliyan 15.3 (a shekara ta 2022) ke rayuwa a Legas.[2] Garin Legas na da mutane kimanin 23.5 million a shekara ta 2018, wanda ya maida shi babban birni mafi girma a nahiyar Afirka. Legas ya kasance cibiyar kasuwanci a jihar Legas da Najeriya gaba daya.[3][4] Legas tana daya daga cikin birane goma masu habbaka da sauri a duniya[5][6]Babban birnin yana matsayin na hudu a kawo kudin shiga (GDP) a Africa[7]kuma akwai daya daga cikin tashar jiragen ruwa mafi hada-hada Afirka.[8]Birnin Legas cibiya ne na ilimi, gargajiya a sassan Afirka da ke kudancin sahara.

Legas a da gida ne ga mutanen Awori, wani reshe ne na Yarbanci na yammacin Afirka. Amma yanzu ta zama birnin tashoshin jiragen ruwa wanda ya samo asali daga tsibirai dabam-dabam.[9]

Gwamnatin tarayya ke gudanar da harkokin wannan babban birni har izuwa shekarar 1967 lokacin da aka rarraba birnin zuwa kananan hukumomi 7 da muke da su a yau.[10][11] da kuma karin birane 3 wanda ya sa kananan hukumomin suka koma 13 wanda suka samar da jihar Legas na yau.[12][13]

Har wa yau, an mai da Ikeja ta zamo babban birnin jihar a shekara ta 1976, sannan Abuja ta koma babban birnin tarayya a shekara ta 1991. Wuraren da ake kira birnin Legas watau "Lagos Metroplitan Area"[14] [15][16]sun hada da manyan biranen[17] jihar guda 16 har da Ikeja. Wannan manyan birane sun mamaye kashi 37% na fadin kasar Legas, sannan tana dauke da fiye da kaso 86% na mutanen jihar Legas.

Akwai rudani game da ainihin yawan mutane birnin Legas. A kidaya da akayi na shekara ta 2006 ya nuna cewa akwai adadin mutane miliyan 8 a birnin. Sai dai gwamnatin jihar ta nuna rashin amincewarta ga adadin kidayan inda ta daki nata adadin da kimanin mutane miliyan 16. A shekara ta 2015 wani kundi wanda gwamnati bata tantance shi ya sanya mutanen Legas har zuwa kusa da jihar Ogun kimanin mutum miliyan 21.[18][19][20]

  1. World's fastest growing cities and urban areas from 2006 to 2020, by CityMayors.com
  2. "Population". Lagos State Government. 2011. Archived from the original on 18 October 2015. Retrieved 3 November 2012.
  3. John Campbell (10 July 2012). "This Is Africa's New Biggest City: Lagos, Nigeria, Population 21 Million". The Atlantic. Washington DC. Retrieved 23 September 2012.
  4. The Most Populated Cities of the World. World Megacities - Nations Online Project". nationsonline.org. Retrieved 23 September 2021
  5. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2021-04-20. Retrieved 2020-03-29.
  6. https://www.britannica.com/place/Lagos-Nigeria
  7. "These cities are the hubs of Africa's economic boom". Big Think. 4 October 2018. Retrieved 23 April 2019.
  8. "Lagos | City, Population, & History | Britannica". britannica.com. Retrieved 19 November 2021.
  9. "CASE STUDY OF LAGOS" (PDF). Archived from the original (PDF) on 4 March 2016. Retrieved 27 November 2015.
  10. "A Flood-Free Lagos: The Regional Imperative". Retrieved 27 November 2015.
  11. Olukoju, Ayodeji (1996). "The Travails of Migrant and Wage Labour in the Lagos Metropolitan Area in the Inter-War Years". Labour History Review. Liverpool University Press. 61: 49–70. doi:10.3828/lhr.61.1.49. Retrieved 27 November 2015.[permanent dead link]
  12. "Lagos State Information". National Bureau of Statistics. Archived from the original on 9 November 2015. Retrieved 25 October 2015.
  13. "Population - Lagos State". Lagos State Government. Archived from the original on 18 October 2015. Retrieved 27 November 2015.
  14. A Flood-Free Lagos: The Regional Imperative". Retrieved 27 November2015.
  15. "Olukoju, Ayodeji (1996). "The Travails of Migrant and Wage Labour in the Lagos Metropolitan Area in the Inter-War Years". Labour History Review. Liverpool University Press. 61: 49–70. doi:10.3828/lhr.61.1.49. Retrieved 27 November 2015.
  16. "Lagos Metropolitan Area: Scope and scale of the shelter problem". Retrieved 27 November 2015.
  17. "Administrative Levels - Lagos State". Nigeria Congress. Archived from the original on 25 December 2005. Retrieved 27 November 2015.
  18. Metro Lagos (Nigeria): Local Government Areas". City Population. 21 March 2015. Retrieved 26 October 2015.
  19. "Population". Lagos State Government. 2011. Archived from the original on 18 October 2015. Retrieved 3 November 2012.
  20. Pacetti, M.; Passerini, G.; Brebbia, C.A.; Latini, G. (2012). The Sustainable City VII: Urban Regeneration and Sustainability. ISBN 9781845645786.

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search