Shafi`iyya

Shafi`iyya
Mai kafa gindi Imam Al-Shafi'i
Classification
Sunan asali المذهب الشافعي

Shafi'iyya, (Larabci|شافعي | Shāfiʿī, ko kuma Shafei) mazhaba ce daga cikin manyan Mazhabobin addinin musulunci guda hudu (4) da ake dasu, wadanda ake amfani da su wurin fayyace dukkan wani fiqhun addinin musulunci, wadanda al'ummar ahlus-sunnah ke bin tafarki akai. [1] Kuma Mazhaban ta samu ne sanadiyar babban Malamin nan, wato AlShaykh Imam Al-Shafi'i, shi kuwa ya kasance daya daga cikin daliban Babban malami Imam Malik, a farkon Karni na 9th.[2] sauran Mazhabobi ukun su ne; Hanafiyya, Malikiyya da kuma Hanbaliya.

Mazhabar Shafi'iyya ita ma ta dogara ne akan Kur'ani da Hadisai ne wurin kafa hujja ko kiyasi a Shari'ar musulunci.[2][3] A inda kuma aka samu wasu ayoyin Qur'ani ko a wasu Hadisai,to Mazhabar Shafi'iyya tana bin Ijma'ine wato abinda ya kasance aka samu mafiya yawan Sahabbai ko Malaman dake a Lokacin sa suke kai.[4] idan kuma ba a samu ijma'i ba to Mazhabar Shafi'iyya takan yi amfani da Ijtihadin Sahabban Manzon Allah, ta amfani da wanda yafi kusa da wannan mas'alar.[2]

Mazhabar Shafi'iyya ta kasance tun a farkon addinin musulunci ita ce take da yawan mabiya, duk da cewar tazone a bayan Mazhabar Hanafiyya da Malikiyya. Amma saidai samun karfi da fadadan Daular Usmaniyya (Ottoman Empire) sai ta rika canja duk Daular da take mulka zuwa bin Malik Hanafiyya.[3] daya daga cikin manyan banbancin da take tsakanin Shafi‘iyya da Hanafiyya shi ne Shafi‘iyya bata yarda da IstihsanI ba a matsayin hanyar samun dokokin addinin musulunci ba, saboda hakan yadogara ne akan yarda da kuma ikon Dan Adam Malik kawai a dokan.[5]

Mazhabar Shafi‘iyya ana samunta a yanzu a kasashe kamar Somaliya, Eritrea, Ethiopia, Djibouti, gabashin Egypt, da Swahili coast, Hijaz, Yemen, Kurdish regions of Gabas ta tsakiya, Dagestan, Chechen da Ingush da kuma yankunan Caucasus, Indonesia, Malaisiya, Sri Lanka, Maldives, Kerala da kuma yankunan gabar Indiya, Singapore, Myanmar, Thailand, Brunei, da Filifin.[6].

  1. Cite error: Invalid <ref> tag; no text was provided for refs named asaeed
  2. 2.0 2.1 2.2 Hisham M. Ramadan (2006), Understanding Islamic Law: From Classical to Contemporary, Rowman Altamira, ISBN|978-0759109919, pp. 27-28
  3. 3.0 3.1 Shafi‘iyyah Bulend Shanay, Lancaster University
  4. Syafiq Hasyim (2005), Understanding Women in Islam: An Indonesian Perspective, Equinox, ISBN|978-9793780191, pp. 75-77
  5. Wael B. Hallaq (2009), Sharī'a: Theory, Practice, Transformations, Cambridge University Press, ISBN|978-0521861472, pp. 58-71
  6. Jurisprudence and Law - Islam Reorienting the Veil, University of North Carolina (2009)

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search