Shi'a

Shi'a
Classification
Sunan asali الشِّيعَة
Branches Ƴan Sha Biyu
Zaidiyyah (en) Fassara
Isma'ilism (en) Fassara
Ghulat (en) Fassara
Zanen sunan Sayyadina Aliyu Wanda aka rubuta shi da jerin sunayen Imaman Shi'a guda goma sha biyu cikin harahen larabci Imamai sune wadanda yan shi'a Imamiyya suke dauka a matsayin jagororin su na addini

Shi'a (larabci شيعة Ko Shi'ah, Bangare, daga Shi'atu Ali ma'ana bangaren Sayyadina Aliyu) bangare ne a addinin Musulunci wanɗanda mabiyansa suka yi amanna da cewa shi ne Halifa na farko bayan manzon Allah (s.a.w) wanda hakan ya sha babban da fahimtar Sunnah ko mabiya aƙidar sunnah "Sunni Islam" waɗanda suka yi imani da cewa ba Ali ne Halifa na farko ba. Suka ce Halifa na farko shi ne Sayyadina Abubakar (R. A). Hujjar mabiya aƙidar Sunnah kuwa ita ce da yake Manzon Allah (s.a.w) bai nuna wani ba wanda za'a bi bayansa sai suka yanke hukuncin yin Shura (wato kuri'a tsakanin al'umma) bayan Wafatin, wato rasuwar Annabi (s.a.w) kuma suka zaɓi Sayyadina Abubakar a matsayin Jagoran daular musulunci kuma jagoran Musulmai. Shi’a na ganin akasin hakan, inda suke cewa Manzon Allah (saw) ya ɗaga hannun Sayyidi Ali a Ranar Ghadeer kuma ya ce duk wanda yake masoyinsa ko majiɓincin lamarinsa to shi ma Ali ya kasance majiɓincin lamarinsa. [1]

Shi'a ita ce ɓangare na biyu a ɓangarorin Musulunci wanda yafi yawan mabiya musamman a yankuna gabas ta tsakiya, bayan ɓangaren Sunna. A ƙididdigar da aka yi a shekarar dubu biyu da tara 2009 ƴan shi'a nada kaso 10-13% na al'umar musulman duniya. Shi'a ƴan sha biyu ko (Ithna ashariyya) su ne suka fi yawa daga cikin ƴan shi'a inda suke da kaso 85% na mabiya mazhabin shi'a a kididdigar shekarar dubu biyu da goma sha biyu 2012.

Duk da haka akwai rabe-rabe masu yawa a shi'a, amma an fi sanin guda uku wato 'Yan sha biyu, Ismailyya da kuma Zaidiyya, amma ƴan sha biyu su ne mafiya yawa daga cikin ɓangarorin shi'a.

  1. https://en.m.wikipedia.orgview_html.php?sq=Andrew_Sorkin&lang=ha&q=Event_of_Ghadir_Khumm

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search