![]() | |
---|---|
national coat of arms (en) ![]() | |
![]() | |
Bayanai | |
Farawa | 20 Mayu 1960 |
Applies to jurisdiction (en) ![]() | Najeriya |
Depicts (en) ![]() |
Costus spectabilis (en) ![]() ![]() |
Tambarin Najeriya ko Kan Sarki wata alama ce gwamnatin Najeriya take amfani da ita a hukimance a matsayin hatin kasa. Tambarin na dauke da hotuna kamar haka; Akwai Mikiya daga sama, tana nuni da karfin Najeriya, sai fararen dokuna biyu a gefe da gefe, suna nuna martabar Najeriya, akwai kuma zane biyu daya daga hagu dayan daga dama sun hade a waje guda, suna nuna kogunan Neja da na Benue da mahadar su a Lokoja. Wannan bakin da zane yabi ta kansa kuma yana nuna albarkatun kasar da Najeriya ke dashi ne. Koriyar ciyawa ta kasa kuma na nuna arzikin Najeria.[1]
Jar fulawa ta ciki na nuna fulawar Najeriya Costus spectabilis, anzabi wannan fulawar ne saboda ana samun ta a ko'ina a sassan Najeriya.
© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search