2 results found for: “Kharkiv_battle”.

Request time (Page generated in 0.4277 seconds.)

Sinimar kasar Ukraine

aka gudanar a Kyiv (1997-) Kharkiv Siren Film Festival, bikin kasa da kasa na gajerun fina-finai, wanda aka gudanar a Kharkiv (2008-) Wiz-Art, International...

Last Update: 2024-03-22T11:21:02Z Word Count : 3442

View Rich Text Page View Plain Text Page

Sinimar kasar Ukrain tun daga samun 'yancin kai

Oleksii Saltykov Олексій Салтиков 1992 Hlasnist-5 Producer's Cooperative (Kharkiv) Виробничий кооператив «Гласність-5» (Харків) Daphnis and Chloe Dafnis...

Last Update: 2022-10-04T01:54:57Z Word Count : 1746

View Rich Text Page View Plain Text Page

Main result

Sinimar kasar Ukraine

Sinima na Ukrainian ya ƙunshi fina-finai na fasahar da shirye-shirye na kirkira wadanda aka shirin a cikin kasar Ukraine ko kuma masu shirya fina-finai na Ukrain a kasashen ketare. Duk da tarihin muhimmanci da kuma kayatattun shirye-shiyensu, akwai jayayya da dama aka matsayin kafar shirye-shiryen, dangane da tasirin Russia da Kasashen turai ga sinimar. Furodusoshin sinimar Ukraine na ayyuka na hadin gwiwa a kasashe daban daban, yayin da darektoci, jarumai da kuma ma'aikatan shiri na fitowa a fina-finan Russia (Soviet Union a da). Fina-finan da suka samu karbuwa sun kasance game da mutanen kasar Ukraine ne, labaransu ko kuma wami al'amari da ya faru, kamar su Battleship Potemkin, Man with a Movie Camera, da kuma fim din Everything Is Illuminated. Ma'aikatar shirya fina-finai ta Ukraine wato Ukrainian State Film Agency ke da alhakin kula da cibiyar National Oleksandr Dovzhenko Film Centre, fannin kula da kwafan fina-finai da kuma tattara su. Wani bikin fina-finai da ake kira Molodist wanda ake yi a birnin Kyiv shi kadai ne biki na ƙasa da ƙasa da aka yarje mawa wanda ake gudanarwa a kasar Ukraine, sashin gasar ya hada da sashin fina-finan dalibai, gajerun fina-finai na farko-farko, da kuma fina-finan hadin gwiwa na sassa daban daban na duniya. Ana gudanar da bikin ne a watan Oktoba na kowacce shekara. Kasar Ukraine tana da tasiri matuka ga sinimar ta Ukraine. Shahararrun daraktocin Ukraine sun hada da Oleksandr Dovzhenko, Dziga Vertov da Serhiy Paradzhanov. Ana kuma ambatan Dovzhenko sau da yawa a matsayin ɗaya daga cikin mafi mahimmancin masu shirya fina-finai na lokacin yankin Soviet da ya gabata, da kuma kasancewa majagaban shirin Soviet montage theory da kafa Dovzhenko Film Studios, sai kuma Sergei Paradzhanov wani darektan fina-finai na kasar Armeniya kuma mawaki wanda ya ba da gudummawa da dama ga sinimar kasar Ukraine, da ta Armeniya da kuma sinimar kasar Georgia. Ya kuma ƙirƙiri nasa salon sinimar, wakokin sinimar ta Ukrainian, wanda sun sha bambam da gundarin ka'idodin gurguzanci na kasar. Yawancin 'yan wasan kwaikwayo na asalin Ukrainian sun sami shahara a duniya da nasara masu tasiri matuka, ciki har da Vira Kholodna, Bohdan Stupka, Sergei Makovetsky, Mike Mazurki, Natalie Wood, Danny Kaye, Jack Palance, Milla Jovovich, Olga Kurylenko da Mila Kunis.


© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search