Umudike ƙauye ne da ke garin Oboro, ƙaramar hukumar Ikwuano a jihar Abiya, Najeriya. Yana da kimanin kilomita 11 daga kudu maso gabas da Umuahia, babban birnin jihar. Garin gida ce ga Jami'ar Aikin Gona ta Michael Okpara da Cibiyar Binciken Tushen Amfanin Gona ta ƙasa. Umudike ya ƙunshi al'ummomi biyu masu cin gashin kansu waɗanda su ne Umudike da Umudike Ukwu. Garin na kewaye da wasu al'ummomi da ke makwabtaka da su inda yake da ra'ayi ɗaya da kuma dabi'un zamantakewa da al'adu. Makwabtan garuruwan sun haɗa da; Umuariaga, Amaoba, Amawom, Nnono, Ndoro and Ahuwa. Waɗannan garuruwan suna ɗaukar kusan kashi 50% na daliban Jami'ar Michael Okpara.
© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search