Abuja

Abuja


Wuri
Map
 9°03′20″N 7°29′29″E / 9.0556°N 7.4914°E / 9.0556; 7.4914
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya
First-level administrative division (en) FassaraBabban Birnin Tarayya, Najeriya
Babban birnin
Yawan mutane
Faɗi 1,235,880 (2011)
• Yawan mutane 1,733.35 mazaunan/km²
Labarin ƙasa
Yawan fili 713,000,000 m²
Altitude (en) Fassara 360 m
Bayanan tarihi
Ƙirƙira 1828
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Wasu abun

Yanar gizo fcta.gov.ng
babban coci a garin abuja
Abuja-college.jpg
Abuja millennium park

Abuja[1] Itace babban birnin tarayya, kuma na takwas a girma a Najeriya[2]. Birnin na nan a tsakiyar ƙasar Najeriya, a cikin Birnin Tarayya (FCT), kuma tsararran birni ne da aka zana a tsakanin shekarun 1980s wanda mai zane Architect Kenzo Tange ya zana ta.[3] Ta zama babbar birnin Najeriya bayan tsohuwar babban birnin Legas[4] a ranar 12 ga watan Disamba shekara ta Alif 1991 .[5]

Birnin ya koma na tarayya ne tun a lokacin mulkin Gen. Ibrahim Babangida[6] a shekarar alif ɗari tara da casa'in da ɗaya (1991)[7] wanda kafin lokacin birnin tarayyar ya kasance a birnin Legas[8] dake kudu maso yammacin Najeriya. Birnin Abuja ya kasance birni ne gagara-misali saboda birnin ya ƙunshi abubuwa da dama wanda ido ne kaɗai zai iya tabbatar da haka. Manƴan Ma'aikatu, Makarantu[9], filayen jiragen sama, da kuma filin wasa Babba, da dai sauran manya-manyan ma'aikatun gwamnati wanda suke juya akalar ƙasar baki ɗaya. A cikin birnin Abuja akwai mutane a kalla 776,298 a kiɗayar shekarar 2006, kasan cewar birnin na tarayya[10] ne wato ya tara duk jinsin mutane[11] da ƙabilun[12] dake Najeriya gaba ɗaya, ko wacce jiha a Najeriya tana da wakilai a sassa daban-daban a cikin Abuja domin ganin sun wakilci jihar su a fage da dama don cigaban jihar su. A cikin birnin Abuja akwai wuraren shaƙatawa da dama da wuraren buɗe ido musamman ga baƙi, waɗanda suke muradin kashe kwarkwatar ido ta fagen kallon abubuwan ban al'ajabi, da ɗebe kewa.

Babban al'amari game da labarin ƙasa na Abuja (wato geography) sun haɗa da Aso Rock[13], gidan shugaban ƙasa (presidential complex), Majalisar dokoki (National assembly),[14] Kotun ƙoli (supreme court), Sannan yawancin birnin ya mike har zuwa kudancin dutsen, Sannan kuma Zuma Rock[15] wanda ke arewacin birnin a bisa babban titin Kaduna.[16]

Manyan wuraren bautan sun haɗa da babban masallaci[17] da babban chochi na birnin Abuja, wato Nigerian National Central Mosque da Nigerian National Christian Centre. Birnin na hada-hada daga filin jirgin saman Abuja wato Nnamdi Azikiwe International Airport. Abuja tana ɗaya daga cikin manyan birane da aka tsara kuma ɗaya daga cikin mafi arziƙi.[18]

Abuja itace cibiyar gudanarwa da siyasa na Najeriya. Har wayau tana ɗaya daga cikin manyan biranen na Afurka musamman matsayin Najeriya a harkokin siyasa da ci gaba.[19] Abuja tana da mahimmanci a harkokin ganawa watau meeting kamar 2003 Commonwealth Heads of Government meeting da kuma 2014 World Economic Forum (Africa) meetings.[20][21]

  1. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://dailytrust.com/minimum-wage-governors-emergency-meeting-kicks-off-in-abuja/&ved=2ahUKEwjYzaXC-PqGAxXZRkEAHfCqD3cQxfQBKAB6BAgsEAE&usg=AOvVaw3eI6Yzjz4joThFGhvxVhCk
  2. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://punchng.com/nigeria-to-install-terrestrial-fibre-optic-infrastructure-edun/%3Famp&ved=2ahUKEwjfu8v1-PqGAxUWT0EAHXxpAfwQyM8BKAB6BAgKEAI&usg=AOvVaw3-Av8oGTAPLbKNZqpUfkXX
  3. "Life of poverty in Abuja's wealth". news.bbc.co.uk. BBC News, Tuesday, 13 February 2007. 2007-02-13. Retrieved 2007-08-10.
  4. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://hausa.legit.ng/news/1598418-ana-fama-da-tsadar-rayuwa-gwamnatin-legas-ta-kwace-motoci-kimanin-40-ta-bayyana-dalili/&ved=2ahUKEwjRsamO-fqGAxUdX0EAHY15CFwQxfQBKAB6BAgGEAI&usg=AOvVaw2HHG4B3BnU2aIP0dR1gKde
  5. Roman Adrian Cybriwsky, Capital Cities around the World: An Encyclopedia of Geography, History, and Culture, ABC-CLIO, USA, 2013, p. 2
  6. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://guardian.ng/the-babangida-leadership-prescription/&ved=2ahUKEwjCtPDm-fqGAxXnT0EAHfSBDtwQxfQBKAB6BAgNEAI&usg=AOvVaw2PE_kvWnIeL0xUJSp-JQNj
  7. https://www.blueprint.ng/as-abuja-millennium-park-reopens/
  8. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://hausa.leadership.ng/yajin-aiki-%25C6%2599ungiyar-%25C6%2599wadago-ta-rufe-filayen-jirgin-saman-legas-da-abuja/&ved=2ahUKEwibl-Ok-vqGAxXGTUEAHaoLAsQQxfQBKAB6BAgMEAI&usg=AOvVaw2s64GFONl9RO9mrE6eka7J
  9. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.bbc.com/hausa/articles/cyrlpz03jp4o.amp&ved=2ahUKEwiyuP7K-vqGAxUiSEEAHZr4DpMQyM8BKAB6BAgLEAI&usg=AOvVaw1NLqlP-s1a7Q2bm8FpTfzu
  10. "Tarihin kafuwar Najeriya tun shekaru aru-aru" http://www.bbc.co.uk/hausa/news/2010/09/100914_early_history_nigeria50.shtml
  11. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://hausa.legit.ng/news/1599342-mutane-sun-barke-da-murna-a-zamfara-bayan-dogo-gide-ya-dawo-yankinsu-sun-rera-masa-waka/&ved=2ahUKEwibtarx-vqGAxX0XUEAHSn_BcsQxfQBKAB6BAgFEAI&usg=AOvVaw0V8RJr3NIYs95kyUktuPqy
  12. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://amp.dw.com/ha/fafutukar-samar-da-zama-lafiya-a-kaduna/a-54693251&ved=2ahUKEwjPyrGW-_qGAxXaWkEAHaAtAfsQyM8BKAB6BAgPEAI&usg=AOvVaw2nWaW9k2lTU_wPxPGHR5u7
  13. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.vanguardngr.com/2024/06/tinubu-presides-over-fec-in-aso-rock/amp/&ved=2ahUKEwjqi_zI-_qGAxWERUEAHV3ODhYQyM8BKAB6BAgFEAI&usg=AOvVaw3MS-l8XZ8-gkTVWndjXxOj
  14. National Assembly | Federal Republic of Nigeria". www.nassnig.org. Retrieved 30 May2020.
  15. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.thecable.ng/iswap-claims-responsibility-for-attack-on-military-checkpoint-near-zuma-rock/&ved=2ahUKEwjH1c7v-_qGAxVmQ0EAHSQZD_kQxfQBKAB6BAgJEAI&usg=AOvVaw3q5aZ-fZJk5bybIDdiub70
  16. Zuma Rock". Visit Nigeria Now. Retrieved 4 January 2022.
  17. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.bbc.com/hausa/articles/ce9dg7z4qvyo.amp&ved=2ahUKEwiwr96V_PqGAxUhUUEAHVqTBy0QyM8BKAB6BAgGEAI&usg=AOvVaw0DG74-QvUbFX0WVt9-KApN
  18. Murray, Senan. "Life of poverty in Abuja's wealth." BBC. Tuesday 13 February 2007. Retrieved 12 September 2011.
  19. The Nigeria Capital City – AMLSN – Salt City 2020". Retrieved 23 January 2021.
  20. The Nigeria Capital City – AMLSN – Salt City 2020". Retrieved 12 May 2020.
  21. Aso Rock Declaration on Development and Democracy: Partnership for Peace and Prosperity | The Commonwealth". thecommonwealth.org. Retrieved 30 May 2020.

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search