Ahmadiyya

Ahmadiyya
Bayanai
Iri ma'aikata
Ƙasa Punjab (Indiya), British Raj (en) Fassara da Indiya
Tarihi
Ƙirƙira 1889
Wanda ya samar
alislam.org
Liwa-e-Ahmadiyya, Tutar Ahmadiyya
Mirza Ghulam Ahmad

Ahmadiyya (Urdu احمدیہ Ahmadiyya) tafiyar imani ce ta addini wadda aka kafa ta a karni na (19), Mirza Ghulam Ahmad ne wanda mabiyan sa suka hakikance kan cewar shine Mahdi ya kafa tafiyar. An kafa tafiyar ne tun kafin Indiya ta rabu zuwa wannan Indiyar ta yanzu wato rabewar ta da Pakistan da Bangladesh.

Ahmad yaso ya sabunta Musulunci, tare da da'awar dawo da ainahin koyarwa ta addinin Musulunci.a shekara ta alif( 1914), tafiyar ta rabe zuwa gida biyu, a sakamakon wanda zai zamo magajin Ahmad kuma har yanzu wadannan bangarorin sunanan. Mirza Ghulam Ahmad yayi da'awar cewa ya cika annabatar Mahdi. Ana yi masa lakani da Mujaddadi na karni na( 14), kuma Yesun da aka alkawarta zuwan sa.[1][2][3][4][5]

Yan Ahmadiyya na daukar kansu a matsayin Musulmai kuma suna da'awar sunayin addinin Musulunci ne wanda Annabi Muhammad ya koyar. Mirza Ghulam Ahmad ya kafa tafiyar ne a shekara ta alif(1889 ), kuma ya saka mata suna Ahmadiyya Muslim Jamaat Fatan sa shine ya dawo da ruhin Musulunci. .

Ainahin tafiyar Ahmadiyya ya tsage zuwa gidaje biyu[6] bayan rasuwar Nooruddin,magajin Ghulam Ahmad na farko.

Wadannan tafiyoyin biyu sune Jama'ar Ahmadiyya da kuma Jama'ar Ahmadiyya ta Lahore (Ahmadiyya Anjuman Ishaat-i-Islam, AAIIL). Bangarorin nada bambanci ga hanyar koyarwa a tsakanin su.[6][7]

Babban bangare na Jama'ar Ahmadiyya na da rassa a sama da kasashen duniya (190), babbar cibiyarta na a birnin Landan na Ingila. Karamin tsagin kuma da akafi sani da Jama'ar Ahmadiyya na Lahore nada cibiya a Lahore, kuma anfi sanin su a Jamani, Autraliya da Pakistan.

Abinda ke kawo rigima shine fahtar Ahmadiyya dangane da rasuwa da dawowar Annabi Isah da kuma mahangar su ga Jihadi. Hakanan ma Yan Ahmadiyya Nada bambancin fahimta da ayar nan ta Kur'ani( 33:40. ), Wannan aya tana magana akan cewa Annabi Muhammad shine cikamakon Annabawa. Sai dai mabiya Jama'ar Ahmadiyya ta Lahore basu da taraddadi dangane da wannan batun domin su basu kallon Mirza Ghulam Ahmad matsayin Annabi. A wannan dalilin ne yasa sukafi kusanci da akidar Musulunci.

Yan Ahmadiyya sun fassara Kur'ani da dukkannin manyan harsunan duniya. Kuma suna yada akidun su da da'awar su awa (24), a tashoshin su na talabijin din su wadanda suka hada da, MTA 1,MTA 2, MTA 3 (domin Larabawa masu kallo) kuma kwanannan suka kaddamar da sabuwar tashar MTA Africa. Yan Ahmadiyya na samar da malamai, likituci,masu kare yancin Dan Adam a kasashen da suka cigaba.

  1. “The Fourteenth-Century's Reformer / Mujaddid”, from the “Call of Islam” Archived 2017-05-18 at the Wayback Machine, by Maulana Muhammad Ali
  2. Claims of Hadhrat Ahmad,Chapter Two
  3. Reflection of all the Prophets
  4. Future of Revelation, Part 7
  5. The Removal of a Misunderstanding
  6. 6.0 6.1 ""The Split in the Ahmadiyya Movement"by Maulana Muhammad Ali". Archived from the original on 2021-04-12. Retrieved 2019-12-19.
  7. ""Refutation of Maulvi Muhammad Ali's Account of Ahmadiyya Dissensions"". Archived from the original on 2007-10-15. Retrieved 2019-12-19.

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search