Bola Tinubu

Bola Tinubu
shugaban ƙasar Najeriya

29 Mayu 2023 -
Muhammadu Buhari
Gwamnan Legas

29 Mayu 1999 - 29 Mayu 2007
Mohammed Buba Marwa - Babatunde Fashola
mamba a majalisar dattijai ta Najeriya

Rayuwa
Cikakken suna Bola Ahmed Tinubu
Haihuwa Lagos, 29 ga Maris, 1952 (72 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Ƴan uwa
Mahaifiya Abibatu Mogaji
Abokiyar zama Oluremi Tinubu
Karatu
Makaranta Chicago State University (en) Fassara
Harsuna Turanci
Yarbanci
Sana'a
Sana'a accountant (en) Fassara da ɗan siyasa
Employers Arthur Andersen (en) Fassara
GTE (en) Fassara
Deloitte (en) Fassara
Mobil Producing Nigeria (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci
Jam'iyar siyasa Alliance for Democracy (en) Fassara
Action Congress of Nigeria (en) Fassara
All Progressives Congress
Dr Adekunle olayinka with president bola Ahmed tinubu
Asiwaju bola Ahmed tinubu
Bola Tinubu Da Foreign Secretary James Cleverly
Bola Ahmed Tinubu Science Complex, Faculty of Science, Lagos State University.jpg

Bola Ahmed Adekunle Tinubu an haife shi a ranar 29 ga watan Maris a shekara ta alif dubu daya da Dari Tara da hamsin da biyu (1952) Miladiyya. Bola Ahmed Adekunle Tinubu ya kasance kwararren dan siyasar Najeriya ne, kuma shugaban kasar Najeriya tun daga ranar 29 ga watan mayun shekara ta 2023.[1] Ya yi aiki a matsayin Gwamnan jihar Legas daga shekarata alif dubu daya da Dari Tara da casa'in da Tara (1999) zuwa shekarata dubu biyu da bakwai (2007), haka yayi Sanata mai wakiltar Legas ta yamma na wani gajeren lokaci a jamhuriya ta uku (Third republic).[2]

Bola Ahmed Tinubu shahararran dan siyasa ne a Najeriya wanda ke da sarautar Asiwaju a kasar Yarabawa, kuma Jagaban a Borgu ta Jihar Neja, ya shahara a fagen siyasa da mulki a Najeriya baki daya.

Ana kallon Asiwaju a matsayin wanda ya dade yana jan zarensa tun daga dawowar Najeriya kan mulkin demokaradiyya ta alif dubu daya da dari Tara da casa'in da Tara (1999), Tinubu ya kasance a matsayin uba a fagen siyasa sakamakon karfin fada a ji da yake da shi a siyasar kasar ta Yarbawa da ma Najeriya baki daya.

Haka kuma ya kafa mutane da dama a Najeriya inda ya yi musu hanya suka samu mukamai a tarayya da jihohi. (Ihayatu ( talk) 21:37, a ranar 30 ga watan Mayu shekarata 2023 (UTC)) [3][4][5]

  1. https://en.m.wikipedia.orgview_html.php?sq=Kharkiv battle&lang=ha&q=Bola_Tinubu
  2. https://punchng.com/tinubu-returns-today-may-present-ministerial-list-after-sallah/
  3. Ewepu, Gabriel (25 October 2019). "CSOs calls on EFCC to investigate Tinubu over alleged money conveyed in bullion vans". Vanguard. Retrieved 22 February 2022.
  4. Olu, Tayo (29 July 2020). "Petition Details Alleged Corrupt Activities Of Tinubu Since 1999". The Whistler. Retrieved 22 February 2022.
  5. Kperogi, Farooq (29 January 2022). "Clarity On Tinubu's Age And Post-Secondary Education". Nigerian Tribune. Retrieved 22 February 2022.

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search