Harshen Swazi

Swazi
siSwati
Asali a Eswatini, South Africa, Lesotho, Mozambique
'Yan asalin magana
L1: Samfuri:Sigfig million (2013–2019)e26
Lamban rijistar harshe
ISO 639-3 ssw
Glottolog swat1243[1]
Swati (Swazi)
Mutum da Swati
Mutane ina Swati
Harshe ina Swati
Ƙasa da Swatini
Rarraba yanki na Swazi a Afirka ta Kudu: adadin yawan mutanen da ke magana da Swazi a gida.
Rarraba yanki na Swazi a Afirka ta Kudu: yawan masu magana da harshen gida na Swazi. 

Swazi ko siSwati yare ne na Bantu na ƙungiyar Nguni da ake magana a Eswatini (tsohon Swaziland) da Afirka ta Kudu da Mutanen Swati. kiyasta yawan masu magana a yankin miliyan 4.7 ciki har da masu magana da harshe na farko da na biyu. Ana koyar da yaren a Eswatini da wasu makarantun Afirka ta Kudu a Mpumalanga, musamman tsoffin yankunan KaNgwane. Siswati yare ne na hukuma na Eswatini (tare da Turanci), kuma yana ɗaya daga cikin harsuna goma sha biyu na Afirka ta Kudu.

Kalmar hukuma ita ce "siSwati" tsakanin masu magana da harshen; a Turanci, Zulu, Ndebele ko Xhosa ana iya kiransa da Swazi . Siswati yana da alaƙa da sauran harsunan Tekela, kamar Phuthi da Northern Transvaal (Sumayela) Ndebele, amma kuma yana kusa da harsunan Zunda : Zulu, Southern Ndebele, Northern Ndebele, da Xhosa .

  1. Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Swati". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search