Harsunan Najeriya

Harsunan najeriya
languages of a country (en) Fassara
Bayanai
Ƙasa Najeriya
Wuri
Harsunan Najeriya

Harsunan Najeriya sun kai harsuna guda 525 na gargajiya da ake amfani dasu a Najeriya.[1][2] Turanci shi ne harshen da ake magana da shi a harkokin gwamnati, harshen turawan mulkin mallaka na ƙasar Birtaniya. Kamar yadda aka rawaito a shekarar 2003, mutane kimanin miliyan 100 suke magana da harshen Turanci da harshen Pidgin na Najeriya a matsayin harshensu na biyu.[3] Harshen Turanci ya fi shahara a yankunan biranen ƙasar fiye da yadda ake amfani dashi a yankunan karkara, saboda cigaba a birane.[4]

Shahararren harshe dangane da yawan masu amfani da harshen shi ne Hausa, mutane aƙalla (fiye da miliyan 49, idan kuma an haɗa da masu amfani da shi a matsayin harshe na biyu, ko L2), Yarbanci (fiye da mutane miliyan 42), Igbo (kimanin miliyan 30), Fulfulde (miliyan 15), Ibibio (miliyan 10), Kanuri (miliyan 8), Tiv (miliyan 4). Miliyan biyu kowane Edo da Igala da Nupe da Ishekiri da Izon da Birom.[5] Tarin harsuna daban-daban na Najeriya yana da dangantaka da wasu harsunan Afirka, kuma harsunan ƙasar sun samo asali ne daga manyan-manyan harsunan Afirka guda uku: Afroasiatic da Nilo-Saharan da kuma Nijar-Congo. Har ila yau Najeriya tana da harsuna da dama da kuma ba a kasafta ba, irin su Centúúm, wanda kuma zai iya wakiltar wani muhimmin bambanci kafin a yaɗa harshe na yanzu.[6]

  1. "Nigeria". Ethnologue. Retrieved 2017-07-14.
  2. Blench, Roger (2014). An Atlas Of Nigerian Languages. Oxford: Kay Williamson Educational Foundation.
  3. "Nigeria". Ethnologue (in Turanci). Retrieved 2018-05-10.
  4. "Vigouroux, Cécile B.; Mufwene, Salikoko S. (2008-11-05). Globalization and Language Vitality: Perspectives from Africa. A&C Black. ISBN 978-1-4411-7073-6.
  5. "Nigeria". worldpopulationreview.com. Retrieved 2020-05-30.
  6. "Adeleke, Dr Wale. "Languages of Nigeria - Regions". NaijaSky. Retrieved 2020-05-27.

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search