Kano

Kano
Wikimedia disambiguation page (en) Fassara
Kano

Kano ( Ajami : كانو) shi ne babban birnin Jihar Kano, kuma yana cikin garuruwa da suke da yawan mutane a jahohin Najeriya mafi yawan al'ummar da ke Arewa maso yammacin ƙasar Najeriya dake yammacin Afrika. Garin ya kasance babban wurin da al'umma ke rayuwa na tsawon dubban shekaru da suka wuce. Shi ne birni na biyu mafi yawan jama'a, yana da yawan jama'a a cikin iyakokin birnin, tare da sama da ƴan ƙasa miliyan huɗu a cikin 5,700km. Yankin gargajiya ne na tsohuwar Daular Dabo mai ƙarni biyu wadanda tun a ƙarni na (19) suka kasance sarakunan gargajiya na cikin gari har zuwa yankin Kano, lokacin da garin ya mamaye daular Biritaniya wato ƙasar Ingila. Majalisar Masarautar Kano ita ce cibiyar masarautar yanzu a cikin iyakokin biranen Kano, kuma ƙarƙashin ikon Gwamnatin Jihar Kano .

Tutar kano ta mussaman

Garin yana karkashin kudu da Sahara, kuma yana daya daga cikin masarautu bakwai na zamani a cikin kasar Hausa kuma manyan mazauna garin su ne aru-aru kafin mulkin mallakar Birtaniya, Kano ta kasance mai cikakkiyar iko da yawan Larabawa, Kanuri, Baburawa da Fulani kuma ta kasance haka tare da harshen Hausa da ake magana da shi a matsayin harshen yare da masu magana da miliyan saba'in a yankin. Addinin Islama ya isa garin a karni na goma sha daya, ko kuma a farkon ta hanyar kasuwancin Sahara kuma sakamakon hakkah ya zama mai wadata kuma cibiyar kasuwanci ta yankin ta Arewacin Najeriya, kuma har yanzu ana danganta ta a matsayin " cibiyar kasuwanci " a arewacin najeriya. Da lakabin da ake mata, "Kano ko da me kazo An fika".


© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search