Matan Annabi

Matan Annabi
group of humans (en) Fassara
Bayanai
Bangare na Ahl ul-Bayt
Depicts (en) Fassara Mata a musulunchi, women in the Qur'an (en) Fassara da female figures in the Quran (en) Fassara
Alaƙanta da Yaran Annabi

Matan Annabi Ta tabbata a cikin nassoshi cewa Annabi Muhammad (S A W) ya aura mata 11 a tsawon rayuwarsa sai dai wasu ruwayoyin sun nuna matansa 13. A Musulunce da kuma duk wani Musulmin kwarai na gari ana kiran su da Ummahati al-Muminin (Larabci: أم ٱلْمُؤْمِنِين; ma'ana 'Uwar Muminai'/Iyayen muminai) ana ambaton su da wannan kalma a matsayin alamar girmamawa, wannan kalmar ta samo asali daga Alqur'ani yazo a cikin Suratul Ahzaab {{النَّبِيُّ أَوْلَى بِالْمُؤْمِنِينَ مِنْ أَنْفُسِهِمْ وَأَزْوَاجُهُ أُمَّهَاتُهُمْ وَأُولُو الْأَرْحَامِ بَعْضُهُمْ أَوْلَى بِبَعْضٍ فِي كِتَابِ اللَّهِ مِنَ الْمُؤْمِنِينَ وَالْمُهَاجِرِينَ إِلَّا أَنْ تَفْعَلُوا إِلَى أَوْلِيَائِكُمْ مَعْرُوفًا كَانَ ذَلِكَ فِي الْكِتَابِ مَسْطُورًا Aya-6.png}} haka kuma Allah madaukakin sarki yana cewa a cikin Alqur'ani { ﴿يَا نِسَاءَ النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِنَ النِّسَاءِ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا ٣٢﴾ [الأحزاب:32.[1][2]

Annabi Muhammad (S A W) ya auri matarsa ​​ta farko, a lokacin da yake da shekara 25 wato Nana Khadija bint Khuwaylid Allah ya kara mata yarda. Sun zauna da ita tsawon shekaru 25 har sai da Allah ya mata rasuwa. Bayan mutuwarta a cikin shekara 619 AD, ya auri mata 10 a cikin sauran shekarun rayuwarsa. Daga cikin wadannan matan biyu suka haifa masa ‘ya’ya: Nana Khadijah da Nana Mariya al-Qibtiyya Allah ya kara yarda da su. Duk matan Annabi sun kasance zawarawa kodai wadda aka saka ko kuma wadda mijinta ya mutu, ban da Aisha bint Abubakar Allah ya kara mata yarda. Baban ta Abubakar bin Abi Quhafa shine Khalifah na farko bayan rasuwar Annabi Muhammad (S A W)

Rayuwar Annabi Muhammad ta kebanta da zamani guda biyu: Makka kafin hijira, birni ne a yammacin kasashen Larabawa, daga shekara ta 570 zuwa 622 Miladiyya, da kuma bayan hijira a Madina, daga 622 har zuwa rasuwarsa a shekara ta 632. Hijira tana nuni ne ga yawan hijirar Fiyayyen halitta Annabi Muhammad da Sahabbansa, wanda akwai hijira ta farko da ta biyu, ta farko itace wadda ysa umurci Sahabbansa da suyi hijira zuwa garin Habasha, sai ta biyu sun tafi garin Madina tareda da abokin sa Abubakar saboda zalunci da musulmi suka fuskanta daga kafiran Makka na wannan lokacin. Bayan wannan hijirar duk an daura aurensa sai biyu.

  1. Aleem, Shamim (2007). "12. Mothers of Believers". Prophet Muhammad(s) and His Family. AuthorHouse. p. 85. ISBN 978-1-4343-2357-6.
  2. Al Kur'ani 33:6

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search