Najeriya

Najeriya
Nijeriya (ha)
Naigeria (ig)
Nàìjíríà (yo)
Tutar Najeriya Tambarin Najeriya
Tutar Najeriya Tambarin Najeriya


Take Tashi Ya Yan Kasa

Kirari «Unity and Faith, Peace and Progress»
«Единство и вяра, мир и прогрес»
«Good people, great nation»
«Undod a Ffydd, Heddwch a Chynnydd»
Official symbol (en) Fassara Costus spectabilis (en) Fassara
Suna saboda Nijar
Wuri
Map
 9°N 8°E / 9°N 8°E / 9; 8

Babban birni Abuja
Yawan mutane
Faɗi 211,400,708 (2021)
• Yawan mutane 228.85 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Bangare na Afirka ta Yamma
Yawan fili 923,768 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Tekun Atalanta
Wuri mafi tsayi Chappal Waddi (2,419 m)
Wuri mafi ƙasa Lagos Island (−0.2 m)
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Taraiyar Najeriya
Ƙirƙira 1 Oktoba 1963
Tsarin Siyasa
Tsarin gwamnati Jamhuriyar Tarayya
Majalisar zartarwa Majalisun Najeriya
Gangar majalisa Majalisar Taraiyar Najeriya
• Shugaban ƙasar Najeriya Bola Ahmad Tinubu (29 Mayu 2023)
Majalisar shariar ƙoli Kotun Koli Ta Najeriya
Ikonomi
Nominal GDP (en) Fassara 440,833,583,992 $ (2021)
Kuɗi Naira
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Suna ta yanar gizo .ng (en) Fassara
Tsarin lamba ta kiran tarho +234
Lambar taimakon gaggawa *#06# da 199 (en) Fassara
Lambar ƙasa NG
Wasu abun

Yanar gizo nigeria.gov.ng
Nigeria w1 locator

Najeriya (/naˈdʒɪəriyə/) ko Nijeriya (/niˈdʒɪəriyə/) da (turanci: Nigeria), A gwamnatance Tarayyar Najeriya, ƙasa ce da ke a Afirka[1] ta Yamma. Tana da iyaka da kasar Nijar[2] daga Arewa da Chadi[3] daga Arewa, maso gabas da Kamaru daga gabas da Benin daga Yamma daga Kudanci kuma tana a gaɓar Tekun Atlantika. Jamhuriyar Tarayyar Najeriya, ta ƙunshi Jihohi guda 36, tare da babban birnin tarayya (Federal Capital Territory) Abuja inda fadar shugaban ƙasa ma'anah billahtake.[4][5][6]

Abuja tana daya daga cikin manyan birane a duniya.[7]

Shopping District
shugaban kasar najeria

Najeriya ta kasance gida da dama ga 'yan asalin Turawa masu mulkin mallaka, jihohin da suka mallaka tunda (BC), tare da Nok Wayewa ta kasance ita ce karo na farko da Turawan mulkin mallaka suka fara mallakewa a Yammacin Africa a cikin karni na sha biyar (15) A zamani jihar an samo asali da Birtaniya a cikin karni na dha tara (19), yana daukar yanayin na yanzu tare da haɗe yankin Kudancin Najeriya da kuma kare Arewacin Najeriya a cikin shekara ta alif dubu daya da ɗari tara da goma sha hudu (1914), ta Lord Lugard. Ingilishi ya kafa tsarin gudanarwa da na doka yayin aiwatar da mulkin kai tsaye ta hanyar shugabannin gargajiya.[8] Najeriya, ta zama ƙasar tarayyar da ke da ƴanci kai tsaye a ranar 1 ga watan Oktoba, shekara ta alif dubu daya da dari tara da sittin (1960). Ta fuskanci yaƙin basasa daga shekara ta 1967, zuwa shekarar 1970, sannan a biyo bayan zaɓaɓɓun gwamnatocin farar hula da mulkin kama-karya na soja, har sai an sami tabbatacciyar dimokuradiyya a shekara ta alif 1999; zaben shugaban kasa na shekara ta 2015, shi ne karo na farko da shugaban Kasa mai ci ya fadi zabensa. [9][10]

Najeriya kasa ce mai yawan Al’umma da ke zaune, sama da kabilu guda Dari, biyu da hamsin (250), wadanda ke magana da yarurruka daban daban guda 500, dukkansu suna dauke da al'adu iri daban daban. Manyan kabilun guda uku su ne Hausa – Fulani a Arewa, Yarbawa a Yamma, da kuma Igbo a gabas, wadanda suka hada da kashi 60% na yawan mutanen. Yaren hukuma shi ne Ingilishi, wanda aka zaba don saukake hadin harshe a matakin kasa. Tsarin mulkin Nijeriya ya tabbatar da ƴancin yin addini ; kuma kasa ce dake dauke da Al’ummar musulmai da Kirista, a lokaci guda. Najeriya ta kasu kashi biyu tsakanin musulmai, wadanda yawanci ke zaune a arewacin kasar, da kuma kiristoci, wadanda yawanci ke zaune a kudancin kasar, tare da ƴan tsirarun da ke yin addinin asali, kamar wadanda ke cikin kabilar Igbo da kuma yarbawa.[11][12]

Bola Tinubu shugaban kasar na yanzu

Najeriya ita ce kasa mafi yawan mutane a Afirka, kuma ƙasa ta bakwai mafi yawan mutane a Duniya, tare da kimanin mutane miliyan 206. Tattalin arzikinta shine mafi girma a Afirka, kuma shi ne na 26, mafi girma a duniya ta hanyar GDP maras fadi, kuma na 25, mafi girma daga PPP. Najeriya galibi ana kiranta da "Giant of Africa", ma'ana karfin Afrika saboda yawan jama'a da tattalin arzikinta, kuma Bankin Duniya yana daukarta a matsayin kasuwa mai tasowa. Karamar yanki ce a cikin Afirka, matsakaiciyar karfi a cikin al'amuran kasa da kasa, sannan kuma tana daya daga cikin kasashe mafi yawan Al’umma a duniya. Koyaya, kasar tana kasa sosai a cikin jerin kasashen duniya, kuma har yanzu tana daya daga cikin kasashe masu rashawa a duniya. Najeriya memba ce ta kafuwar Tarayyar Afirka, kuma memba ce a kungiyoyin kasa da kasa da dama, wadanda suka hada da Majalisar Dinkin Duniya, kungiyar kasashen Yammacin Africa (ECOWAS), kungiyar kasashe masu arzikin man fetur, (OPEC), kuma memba na yau da kullum a gamayyar MINT, kuma tana daya daga cikin Kasashe goma sha daya masu tashen karuwan tattalin arziki wato "Next Eleven".[13]

  1. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.voahausa.com/amp/ecowas-nazari-kan-dalilan-juyin-mulki-a-afirka-ta-yamma-/7337186.html&ved=2ahUKEwjOsPSs6fOGAxWhB9sEHUt2CtwQyM8BKAB6BAgFEAI&usg=AOvVaw2NCWIateDSWwtYCSOo6PrG
  2. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://amp.scmp.com/news/world/africa/article/3267740/coup-hit-niger-was-betting-china-backed-oil-pipeline-lifeline-then-troubles-began&ved=2ahUKEwjWhrzXvvSGAxWHrpUCHXf0D3IQyM8BKAB6BAgFEAE&usg=AOvVaw0IqGnxi9xE7AEs-SbJGSdu
  3. https://www.google.com/url?sa=t&source=web&rct=j&opi=89978449&url=https://www.thehealthsite.com/news/chad-first-country-eliminate-neglected-tropical-disease-2024-african-trypanosomiasis-sleeping-sickness-1102210/amp/&ved=2ahUKEwiowPbwvvSGAxWjpZUCHXrfDzMQyM8BKAB6BAgOEAI&usg=AOvVaw06192SscI8sTJrAnyIhehV
  4. http://www.unep.org/news-and-stories/story/unep-ogoniland-oil-assessment-reveals-extent-environmental-contamination-and
  5. https://www.greenleft.org.au/content/shell%E2%80%99s-nigeria-ecocide-creating-refugee-crisis,%20https://www.greenleft.org.au/content/shell%E2%80%99s-nigeria-ecocide-creating-refugee-crisis[permanent dead link]
  6. https://web.archive.org/web/20141205124719/http://www.punchng.com/news/us-sends-medical-experts-to-study-how-nigeria-contained-ebola/
  7. Muhammadu Buhari
  8. Achebe, Nwando, 1970-. The female king of colonial Nigeria : Ahebi Ugbabe. Bloomington. ISBN 978-0-253-00507-6. OCLC 707092916.CS1 maint: multiple names: authors list (link)
  9. https://www.theguardian.com/society/2015/may/29/outlawing-fgm-nigeria-hugely-important-precedent-say-campaigners
  10. "Buhari wins historic election landslide". Reuters (in Turanci). 2015-03-31. Retrieved 2020-05-25.
  11. https://www.premiumtimesng.com/news/headlines/520849-number-of-poor-people-in-nigeria-to-reach-95-million-in-2022-world-bank.html
  12. https://www.washingtonpost.com/outlook/2019/09/16/official-us-poverty-rate-is-based-hopelessly-out-of-date-metric/
  13. https://www.fao.org/nigeria/fao-in-nigeria/nigeria-at-a-glance/en/

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search