Ogun

Ogun


Suna saboda Kogin Ogun
Wuri
Map
 7°00′N 3°35′E / 7°N 3.58°E / 7; 3.58
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Abeokuta
Yawan mutane
Faɗi 5,217,716 (2016)
• Yawan mutane 307.28 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 16,980.55 km²
Wuri a ina ko kusa da wace teku Bight of Benin (en) Fassara
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Jihar Yammacin Najeriya
Ƙirƙira 3 ga Faburairu, 1976
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa Executive Council of Ogun State (en) Fassara
Gangar majalisa Ogun State House Of Assembly (en) Fassara
• Gwamnan jahar ogun Dapo Abiodun (29 Mayu 2019)
Bayanan Tuntuɓa
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-OG
Wasu abun

Yanar gizo ogunstate.gov.ng
Jihar Ogun
mutanen Ogun
Babbar asibitin ogun
babban masallaci a ogun

Jihar Ogun,Jiha ce dake kudu maso yammacin, Najeriya. Wacce aka ƙirƙira a ranar 3 ga watan Fabrairun shekarar alif 1976, daga yankin jihar yammacin Najeriya. Jihar Ogun tana da iyaka da jihar Lagos daga kudu, jihar Oyo dkuma a Osun daga arewa, jihar Ondo da kuma Jamhuriyar Benin daga yamma. Babban birnin jihar ita ce Abeokuta, kuma ita ce birni mafi girma ta fuskar yawan jama'a. Sauran muhimman birane sun haɗa da, Ijebu Ode babban birnin Daular Ijebu, sai kuma Sagamu (inda aka fi samun goro a Najeriya).[1] Ogun na da yanayi na rain forest da kuma manyan itace daga arewa maso yamma.

Tana da yawan fili kimanin kilomita arba’in 16,980.55[2] da yawan jama’a 3,751,140 (a bisa ƙidayar shekarar 2006). Inda jihar ta zamo ta 16 a yawan jama'a a Najeriya.[3] Gwamnan jihar shi ne Dapo Abiodun na jam'iyyar APC, wanda aka rantsar a ranar 29 ga watan Mayun, 2019, a babban filin wasan ƙwallon kafa na MKO Abiola Stadium dake Kuto, Abeokuta.

Ana mata laƙabi da "Mashigar Najeriy" wato (Gateway of Nigeria), kuma garin ya yi fice da manyan gidajen masana'antu da kuma zama tushen ƙere-ƙere a Najeriya. Sanannun masana'antun jihar sun haɗa da Kamfanin Simintin Dangote dake Ibese,[4] Kamfanin Nestle,[5] Kamfanin siminti na Lafarge dake Ewekoro, Kamfanin Memmcol dake Orimerunmu,[6] Kamfanin Coleman Cables dake Sagamu da Arepo,[7] Kamfanin Procter & Gamble dake Agbara[8] da dai sauransu.

Mafi akasarin mutanen Ogun Yarbawa ne,[9] inda suke amfani da harshen yarbanci a matsayin yaren garin. Addinai dake da mafi yawan mabiya sune Musulunci da Kiristanci, duk da akwai sauran mabiya addinan gargajiya a Jihar.[10] Jihar Ogun ta yi fice a wajen samar da Shinkafar Ofada. Har wayau, jihar Ogun ta kasance gida ga taurari da manyan mutane daban daban a Najeriya da sassan Afurka gaba ɗaya daya.

  1. "Ogun | state, Nigeria". Encyclopedia Britannica. Retrieved 2021-09-23.
  2. "World Gazetteer: Nigeria - administrative divisions (per geographical…". archive.ph. 2013-01-05. Archived from the original on 2013-01-05. Retrieved 2021-12-10.
  3. "Ogun State". Ogun Smart City. Retrieved 2020-05-24.
  4. "Ibese Cement Plant - Dangote Cement". dangote.com. Archived from the original on 11 June 2016. Retrieved 28 May 2017.
  5. "Nestlé Flowergate Factory, Ogun". Food Processing Technology. Retrieved 28 May 2017.
  6. "Electricity Meter Manufacturing Company". www.memmcol.com. Retrieved Aug 6, 2020.
  7. "Coleman Wires and Cables". www.colemancables.com. Retrieved 28 May 2017.
  8. "P&G in Nigeria". www.pgcareers.com. Retrieved 2020-05-24.
  9. "OGUN STATE". Ogun State Government Official Website. Retrieved 2021-03-07.
  10. "Oludare, Ishola (2021-08-15). "Declare public holiday for Ifa festival like Muslims, Christians – Traditionalists tell Abiodun". Daily Post Nigeria. Retrieved 2021-12-08.

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search