Ondo (jiha)

Ondo


Wuri
Map
 7°10′N 5°05′E / 7.17°N 5.08°E / 7.17; 5.08
Ƴantacciyar ƙasaNajeriya

Babban birni Akure
Yawan mutane
Faɗi 4,671,695 (2016)
• Yawan mutane 301.4 mazaunan/km²
Harshen gwamnati Turanci
Labarin ƙasa
Yawan fili 15,500 km²
Sun raba iyaka da
Bayanan tarihi
Mabiyi Jihar Yammacin Najeriya
Ƙirƙira 3 ga Faburairu, 1976
Tsarin Siyasa
Majalisar zartarwa executive council of Ondo State (en) Fassara
Gangar majalisa Majalisar dokokin jihar Ondo
Bayanan Tuntuɓa
Lambar aika saƙo 340001
Kasancewa a yanki na lokaci
Lamba ta ISO 3166-2 NG-ON
Wasu abun

Yanar gizo ondostate.gov.ng
mutanen ondo
Gajeren zance na tarihin Ondo cikin yaren Ondo daga ɗan asali harshen
kasuwa a ondo

Jihar Ondo Jiha ce dake kudu maso yammacin Najeriya. An ƙirƙiri jihar Ondo a ranar 3, ga watan Fabrairun shekara ta 1976, daga tsohuwar yankin Yammacin Najeriya.[1] Ondo na da iyaka da jihar Ekiti (wanda a da tana cikin jihar Ondo ne) daga arewa, Jihar Kogi daga arewa maso gabas, jihar Edo daga gabas, Delta daga kudu maso gabas, Ogun daga kudu maso yamma sannan kuma jihar Osun daga arewa maso yamma sai kuma Tekun Atlantic daga kudu. Babban birnin jihar shi ne Akure, babban birnin masarautar Akure a da.[2] Ondo na da kasafin daji na mangrove-swamp forest kusa da gaɓar Benin.[3]

Ana mata laƙabi da "Sunshine State" wato "jiha mai haskakawa". Jihar Ondo ita ce ta tara a girma a Najeriya.[4] Kuma ita ce jiha ta 25, a faɗin ƙasa.[5] Mafi akasarin mutanen garin yarbawa ne.[6][7] Akasarin mutanen garin yarbawa ne, a yayinda ake amfani da harshen yarbanci a garin. Albarkatun ƙasan Ondo ya ta'allaka ne a kan man fetur, noman cocoa, da makamantansu.[8] Inda tsaunukan Idenre suke, wanda shi ne tsauni mafi girma a yankin yammacin Najeriya.

daya daga cikin manyan makarantu na jihar ondo


Tana da yawan fili kimanin kilomita murabba’in 15,500, da yawan jama’a miliyan uku da dubu dari huɗu da arba'in (ƙidayar a shekara ta 2006). Babban birnin tarayyar jahar shi ne Akure. Oluwarotimi Odunayo Akeredolu, shi ne gwamnan jihar tun zaɓen shekara ta 2011 har zuwa yau. Mataimakin gwamnan shi ne Agboola Ajayi. Dattijan jihar su ne: Yele Omogunwa, Robert Ajayi Boroffice da Omotayo Donald.

Jihar Ondo tana da iyaka da jihohin shida: Delta, Edo, Ekiti, Kogi, Ogun kuma da Osun.

  1. "Ondo Election: 20 things to know about South-west state". 2020-10-09. Retrieved 2022-04-08.
  2. "Ondo | state, Nigeria". Encyclopedia Britannica. Retrieved 2021-09-23.
  3. "Ondo | state, Nigeria". Encyclopedia Britannica. Retrieved 2021-09-23.
  4. http://www.population.gov.ng
  5. "World Gazetteer: Nigeria - administrative divisions (per geographical…". archive.ph. 2013-01-05. Archived from the original on 2013-01-05. Retrieved 2022-04-19.
  6. "The People Of Ondo Kingdom And Their Culture: A Historical Survey And Political Underpinning – Ondo Connects New Era". Retrieved 2021-03-07.
  7. "Geography and Society", The Yoruba from Prehistory to the Present, Cambridge University Press, pp. 1–28, 2019-07-04, doi:10.1017/9781107587656.001, ISBN 978-1-107-58765-6, S2CID 131619880, retrieved 2021-03-07
  8. "Ondo State". Nigerian Investment Promotion Commission. 2019-01-09. Retrieved 2021-03-07.

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search