Sunnah

Sunnah
Asali
Mawallafi Muhammad
Characteristics
Harshe Larabci
Fayil:Al-Haram mosque-Flickr - Al Jazeera English.jpg
Masallacin Harami dake Makkah waje ne na daya mafi tsarki a wajen Musulmi Mabiyan Sunnar Annabi Muhammad (S.A.W.)

Sunnah Shi ne ɓangare mafi girma da tsari daga cikin ɓangarorin addinin Musulunci. Asalin sunan ya zo ne daga kalmar Sunnah, wato koyi da yin dukkan abun da Annabi Muhammad (S.A.W.) ya aikata, ko ya yi umarni, da a aikata ko kuma aka aikata shi a gabansa amma baiyi hani akan abun da aka aikatan ba. Bambanci tsakanin aƙidun Sunnah da kuma na Shi'a ya samo asali ne tun daga taƙaddama a kan wanda ya cancanci ya jagoranci al'umar Musulmi bayan wafatin Annabi (S.A.W.), wato wanda ya cancanci ya yi Khalifanci. A ɓangaren fahimtar mabiya Sunnah sun ce, tunda yake Annabi (S.A.W) bai yi nuni ba da wani cewa shi za'a bi to sai suka yanke hukuncin a bai wa surukinsa wato Sayyadina Abubakar ya zamo Khalifa na farko.

Masallacin sunnah

Amma a ɓangaren Mabiya Shi'a kuwa sai suka ce ai a ranar Ghadir Khumm Annabi (s.a.w) ya sanar da cewa ba wanda zai gaje shi sai ɗan'uwansa kuma sirikinsa wato Sayyadina Ali sun ce saboda shi jininsa ne kuma surukinsa wato mijin ƴarsa, Sayyida Fatima "Bint Nabiy".

Tun daga nan ne rikicin ɓangaren Sunnah dana ɓangaren Shi'a ya samo asali.

A shekarar 2009 Musulmai mabiya Sunnah sun kai 87% zuwa 90%. Haka zalika Mabiya Ɓangaren Sunnah su ne ɓangare a Addini wanda suka fi ko wanne yawa a duniya bayan Katolika a addinin Kiristanci. Sanannu ne a sunan da suka yi fice da shi wato Ahlul Sunnah Wal Jama'a wato (al'umma mabiya sunnah).


© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search