Daular Kanem-Bornu

Daular Kanem-Bornu

Wuri

Babban birni Njimi
Yawan mutane
Harshen gwamnati harsunan sahara
Bayanan tarihi
Mabiyi Kanem Empire (en) Fassara
Ƙirƙira 11 century
Rushewa 22 ga Afirilu, 1900
Tutar daular Kanem Bornu

Daular Kanem–Bornu ta kasance daula ce data taɓa kasancewa a inda ayau itace kasar Cadi da Nijeriya. Masanan ƙasashe larabawa suna kiran daular da Kanem Empire daga ƙarni na 9th har zuwa sanda takasance daular musulunci Bornu (Daular Bornu) a Shekarar 1900. Kanem Empire CE tun daga shekara ta (c. 700 zuwa 1380) takasance ne ƙasashen Chad, Nigeria da Libya.[1] A matuƙar girmar daular ta tattara ƙasashe ba kawai ɗaukacin ƙasar Chad ba, takai har zuwa kudancin ƙasar Libya (Fezzan) da gabashin Nijar, arewa maso gabas din Nigeria da arewacin kamerun. A yayin da Daular Bornu take a shekara ta (1380s zuwa 1893) takasance a inda ake kira ayau arewa maso gabashin Nigeria, wanda tacigaba da girma fiye da daular Kanem, ta tattari kasashen da ayau sune ko kuma suke daga cikin kasashe kamar Chad, Nijar, Sudan, da Cameroon; an samar da’ita daga shekara ta 1380s zuwa shekarar 1893. Farkon tarihin daular an santa ne da jerin masu sarautar ko Girgam matafiyin bincike dan kasar jamus wato Heinrich Barth wanda aka gano a shekarar 1851.

  1. "Kanem-Bornu". Encyclopædia Britannica. Retrieved 24 September 2014.

© MMXXIII Rich X Search. We shall prevail. All rights reserved. Rich X Search